‘Yan Wasan da Suka ci Real da Atletico a La Liga a Bana

 

Ranar Talata za a ci gaba da wasannin mako na 31 a gasar La Liga, inda za a fara da fatawa uku.

Za a buga wasa hudu ranar Laraba, sannan a kammala a karawa uku ranar Alhamis a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Barcelona ta doke Atletico Madrid 1-0 a wasan mako na 30 ranar 23 ga watan Afirilu a Camp Nou.

Daf da hutu ne Ferran Torres ya ci wa Barcelona kwallon da ya ba ta damar hada maki ukun da take bukata.

Dan kwallon ya zama na biyu a Barcelona da ya ci Real da Atletico a La Liga a kakar tamaula, bayan Luis Enrique da ya yi wannan bajintar 2002/03.

A kakar nan ta 2022/23 ‘yan wasa hudu ne suka ci Real Madrid kwallo da kuma Atletico Madrid a gasar ta La Liga.

Torres ya nuna kansa ya shiga sahun manya a cin kwallaye, inda Xavi ke saka shi wasa tare da Raphinha da Robert Lowandowski a matakin masu cin kwallaye.

Sauran ‘yan wasan da suka ci Real da Atletico a kakar nan sun hada da Gerard Moreno da Yéremi Pino daga Villarreal da dan wasan Mallorca Coto Muriqi.

Kawo yanzu saura fafatawa takwas a kammala gasar La Liga ta bana, watakila a kara samun wasu da za su ci Real da Atletico a kakar nan.

Barcelona ce ta daya a teburin La Liga da maki 76, sai Real Madrid ta biyu mai maki 65 da Atletico Madrid ta uku da tazarar maki biyar tsakaninta da kungiyar Santiago Bernabeu.

Wadanda ke karshen teburi kuwa a La Liga sun hada da Valencia mai mako 30 da Espanyol mai maki 28 da Elche ta karshe mai maki 13.

Jerin ‘yan wasan da ke kan gaba a cin kwallaye:

Robert Lewandowski Barcelona 17

Karim Benzema Real Madrid 14

Enes Unal Getafe 13

Borja Iglesias Real Betis 12

Joselu Espanyol. 12

Iago Aspas Celta de Vigo 12

Vedat Muriqi Real Mallorca 12

Antoine Griezmann Atletico Madrid 11

Alexander Sorloth Real Sociedad 10

Alvaro Morata Atletico Madrid 10

Gabriel Veiga Celta de Vigo 9

Martin Braithwaite Espanyol 9

Vinicius Junior Real Madrid 9

Wasanin mako na 31 a La Liga:

Ranar Talata 25 ga watan Afirilu

Cadiz da Osasuna

Girona da Real Madrid

Real Betis da Real Sociedad

Ranar Laraba 26 ga watan Afirilu

Atletico Madrid da Real Mallorca

Getafe da Almeria

Celta Vigo da Elche

Rayo Vallecano da Barcelona

Ranar Alhamis 27 ga watan Afirilu

Valencia da Real Valladolid

Villarreal da Espanyol

Athletic Bilbao da Sevilla

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here