Munfi Amfana da APC Fiye da PDP – Gwamnan Ebonyi

Jihata ta fi samun romon demokradiyya karkashin Buhari fiye Obasanjo, Yar’adua da Jonathan, Umahi.

Ya yi jawabi kwana daya bayan sauya sheka daga tsohuwar jam’iyyar ta PDP zuwa APC.

Umahi ya kasance shugaban jam’iyyar PDP na jihar Ebonyi, sannan yayi mataimakin gwamna, kuma yanzu yana gwamna karo na biyu.

Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya bayyana cewa gwamnatin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta fi alhairi fiye da shekaru 16 da gwamnatin Peoples Democratic Party (PDP).

Umahi ya bayyana hakan a Abuja ranar Juma’a a hirar da yayi a shirin Politics Today na tashar Channels TV.

“Idan ka kwatanta, ina ganin yan shekarun gwamnatin APC sun fi na tsohuwar jam’iyyata. Babu wani mai kama karya kan lamuran jam’iyyar,” Umahi yace.

Umahi ya ce jihar Ebonyi ta amfana da APC cikin shekaru 5 da suka gabata fiye da yadda ta amfana da PDP cikin shekaru 16 da tayi mulki.

“Kowa na da zabi a rayuwa. Na zabi APC saboda suna gudanar da lamuransu da girmama shugaban kasa da kuma adalci ga dukkan gwamnoni,” ya kara.

Wannan jawabi na gwamna ya biyo baya sauya shekar da yayi daga jam’iyyar PDP zuwa APC kuma jiga-jigan APC sukayi masa kyakkyawan tarba.

Wadanda suka halarci taron sauya shekarsa sun hada da tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani; shugaban kwamitin rikon kwaryan APC kuma gwamnan Yobe, Mai Mala Buni; da gwamnan jihar Jigawa, Muhammadu Badaru Abubakar.

Sauran sune gwamnan Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu; gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello, dss.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here