NARD: Za mu yi Amfani da Tsumagiyarmu – Ministan Ayyuka da Kwadago ga Likitoci

 

Gwamnatin Najeriya zata zartar da hukuncin dakatar da biyan likitoci matsawar basu yi aiki ba saboda yajin aikin da suka tsunduma.

Ministan ayyuka da kwadago, Chris Ngige ya bayar da wannan jan kunnen a ranar Juma’a a yayin da ake wata tattaunawa dashi.

A cewar Ngige, ma’aikatar kwadago tana da makaman da za ta yakesu kuma ta hukuntasu matsawar suka ki amincewa da tayin da ya gwamnati zata yi musu ranar Talata Gwamnatin tarayya zata tilasta dokar dakatar da albashi matsawar ma’aikaci bai yi aikinsa ba ga kungiyar likitoci masu neman kwarewa na Najeriya basu koma kan ayyukansu ba.

Ministan ayyuka da kwadago, Chris Ngige ne ya sanar da wannan jan kunnen a ranar Juma’a a wata tattaunawa da gidan talabijin din Channels.

“A ranar Talata, zan gayyacesu don su koma kan ayyukansu. Zan sanar dasu cewa matsawar ba su yi aiki ba gwamnati ba za ta biyasu ba,” cewar Ngige.

“Wadanda aka dauka aiki ya kamata su dage wurin kulawa da lafiyar marasa lafiya.

Za mu iya neman likitocin gargajiya, bana fatan mu kai nan wurin amma in dai aka kai toh za mu yi amfani da tsumagiyarmu.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here