Dalilin da Yasa Muka Amince da Tayin N70,000 a Matsayin Albashi Mafi ƙanƙanta -NLC
Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta NLC sun sanar da amincewarsu da naira 70,000 a matsayin albashi mafi ƙanƙanta ga ma’aikatan ƙasar.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ne ya amince da sabon albashin a ganawarsa da wakilan ƙungiyoyin ƴan ƙwadago na ƙasar a ranar Alhamis.
Wannan na zuwa ne bayan kwashe tsawon lokaci ana taƙaddama tsakanin ƴan ƙwadago da gwamnatin Najeriya game da sabon albashin mafi ƙanƙanta ga ma’aikata.
Read Also:
Shugaban NLC Joe Ajaero ya ce sun amince ne da tayin N70,000 saboda akwai abubuwan da ke ƙunshe da ya kira na ƙarfafa guiwa.
Ƙungiya ta ce abin da ya ƙara ƙarfafa mata guiwa na amincewa da tayin shi ne alƙawalin da shugaban ƙasar ya ɗauka na sake duba albashin duk bayan shekara uku maimakon shekara biyar, kamar yadda mataimakin shugaban Kabiru Adamu Minjibir ya shaida wa manema labarai a fadar shugaban ƙasa.
“Sannan gwamnati za ta bayar da manyan bas bas masu ɗaukar mutum 100 wanda zai rage wa ma’aikata wahalar tafiye-tafiye,” in ji shi.
Tun janye tallafin mai da gwamnatin Bola Tinubu ta yi, ta shiga takun-saka da ƙungiyoyin ƙwadago, inda suka nemi ƙarin albashi da ya zarta kashi 300 cikin 100 sakamakon tsadar rayuwa da janye tallafin ya jefa ƴan Najeriya.