Na Amince da Hukuncin da Aka Dauka a Kai na – Adams Oshiomhole
Tsohon shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole, ya umarci lauyoyinsa da su janye korafin da ya kai kotu.
Oshiomhole ya ce ya amince da hukuncin da aka dauka a kansa na tube shi daga kujararsa, kuma ya gode da damar da aka bashi.
A cewarsa, bai rike wani wanda yayi sanadiyyar cire shi daga mukaminsa a ransa ba, kuma yana alfahari da nasarorin da aka samu a mulkinsa.
Adams Oshiomhole, tsohon shugaban jam’iyyar APC, ya ce idan aka bashi damar shugabantar jam’iyyar ba zai yi ba.
A ranar Litinin, Oshiomhole ya ce yana matukar alfahari da yadda NWC tayi aiki a karkashin mulkinsa, The Cable ta wallafa.
Read Also:
Oshiomhole ya ce bai riki kowa ba a zuciyarsa, har wadanda suka shiga suka fita har aka tumbuke shi daga mukaminsa ba, hasalima ya umarci lauyoyinsa da su janye korafin da ya tura a kan dakatar dashi da aka yi.
“Na umarci lauyoyina da su janye korafin da nayi a kan cireni da aka yi daga mukami na a matsayin shugaban jam’iyya,” kamar yadda takardar tazo.
“Don haka, an gama yanke shawara aka cireni daga mukami na, kuma na amince da hukuncin dari bisa dari wanda aka yanke a kaina.
“Na riga na rufe wannan babin a rayuwata. Ko da kuwa NEC ta canja shawara, ko kuma kotu ta umarci a mayar da ni, zan ki amincewa da komawa kujerar shugaban jam’iyyar APC.
“Ina matukar alfahari da nasarorin da NWC ta samu a karkashin shugabancina, sannan na ji dadin yadda mambobi 18 suka taru, muka yi aiki duk don cigaban jam’iyya.
Sannan kuma, ban rike wani wanda yayi sanadiyyar tubeni daga kujerata ba a rai na.” Oshiomhole ya mika godiyarsa ga shugaba Muhammadu Buhari saboda bashi hadin kai dari bisa dari lokacin yana shugabantar APC.