Jami’an Amotekun a Jihar Ondo Sun Kama ‘Yan Arewa 168
Jami’an tsaro masu zaman kansu a jihar Ondo wadanda aka fi sani da Amotekun sun tsare wasu mutane 168 da ake zargi da kutse a cikin manyan motoci biyu.
Read Also:
Wannan ya zo ne bayan kwanaki uku da kama wasu mutum 151 da su ma ake zargi da kutse cikin jihar, dauke da layu a buhunhunan shinkafa a yankin Sango da ke babban titin Akure-Ado.
Kwamandan jami’an Akogun Adetunji Adeleye ya ce an tare waɗanda ake zargin ne a kusa da al’ummomin Itaogbolu da Iju da ke karamar hukumar Akure ta arewa yayin da ake binciken motoci.
Kamar yadda kwamandan ya bayyana, mutanen da aka kama sun zo ne daga jihohin Kano da Jigawa ba tare da tabbacin me ya kai su jihar Ondo ba.