Gaza: Amurka ta Dakatar da Aika wa Isra’ila Makamai

 

Amurka a makon da ya gabata ta dakatar da aika wa Isra’ila bama-bamai kan fargabar kai munanen hare-hare a birnin Rafah da ke kudancin Gaza…a cewar wani babban jami’in gwamnatin Amurka.

Jami’in ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta CBS cewa kayan sun haɗa da bam mai nauyin tan 1,800 2,000lb da 1,700 500lb.

Ya ƙara da cewa Isra’ila ba ta saurari koken Amurka kan buƙatun kayan agajin da suka kamata a kai wa mutanen Rafah ba.

Mai magana da yawun rundunar sojin Isra’ila ta IDF Daniel Hagari ya shaida wa manema labarai cewa Amurka ta riƙa bayar da taimakon tsaro tun farkon yaƙin, inda ya ƙara da cewa an yi wata tattaunawar sirri tsakanin ƙasashen biyu.

Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare a tsakiyar dare a zirin Gaza sa’o’i bayan sojojin Isra’ila cikin motocin yaƙi sun ƙwace mashigar Rafah da ke ɓangaren Falasɗinawa a kan iyakar Masar.

Yanzu haka dai Isra’ila ta tsananta kai hare-hare a kewayen Rafah. Wasu kafofin sun ce mutum bakwai aka kashe ƴan gida ɗaya a wani hari da aka kai.

Rafah ta kasance muhimmiyar hanya ta shigar da kayan agaji kuma hanya ɗaya da mutane ke iya fita daga garin tun farkon fara yaƙi tsakanin Isra’ila da Hamas a Oktoban shekarar da ta gabata.

An rufe mashigar tun safiyar ranar Laraba amma rundunar sojin ta ce za ta ƙara buɗe mashigar Kerem Shalom da ke kusa da wadda aka rufe tsawon kwanaki huɗu.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here