Amurka na Jagorantar Atisayen Soji na Kwana 15 a Ghana da Ivory Coast
Amurka na jagorantar wani atisayen soji na kwana 15 a ƙasashen Ghana da Cote d’Ivoire.
Atisayen wanda aka fara ranar 1 ga watan Maris ya ƙunshi sojoji 1,300 daga ƙasashe 30 na duniya.
Read Also:
Atisayen wanda aka yi wa laƙabi da “Flintlock 2023” an shirya shi ne da nufin ƙarfafa wa ƙasashen duniya gwiwwa wajen yaƙar ƙungiyoyin ta’addancin tare da haɗin gwiwwa a kan iyakokin ƙasashe.
Tun shekarar 2005 ne Amurka ke jagorantar atisayen soji a yankin yammacin Afirka duk shekara.