Rikicin Sudan: Amurka ta Kwashe Jami’anta Daga ƙasar

Shugaba Joe Biden ya ce sojojin Amurka sun kwashe jami’an ƙasar da kuma iyalansu daga Sudan.

Ya ce ya yi alfahari da jajircewar ma’aikatan ofishin jakadancin ƙasar sannan ya godewa ƙasashen Djibouti da Habasha da kuma Saudiyya waɗanda ya ce sun taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da aikin.

Mayaƙan RSF sun yi aiki tare da sojojin Amurka wajen kwashe Amurkawa kusan 70 da kuma iyalansu daga ƙasar.

Wannan na zuwa ne a yayin da aka shafe kwana 9 ana bata kashi tsakanin sojin gwamnatin Sudan da kuma dakarun RSF.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here