An Hallaka Dubban Fararen Hula a Burkina Faso

Hukumomi a arewacin Burkina Faso sun ce an kashe fararen hula kusan 60 a ƙauyen Karma da ke kan iyaka da ƙasar Mali.

Wani mai shigar da ƙara a yankin ya ce an sanar da shi faruwar lamarin ne ranar Juma’a inda ya ƙara da cewa wasu mutane ne da ke sanye da kakin sojoji suka aiwatar da kisan.

Ko a makon jiya ma, an far wa sojojin Burkina Faso da wasu sojojin sa-kai a yankin da ke kusa da Wahiguya inda mutane kusan 40 suka mutu tare da raunata fiye da 30.

An kashe dubban mutane tun a lokacin da masu tada kayar baya suka fara kai hari a yankin.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here