Amurka ta Magantu Kan Kisan Haniyeh
Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken ya ce, ƙasarsa ba ta da masaniya ko kuma hannu a kisan da aka yi wa Isma’il Haniyeh.
Sakataren harkokin wajen Amurkan, ya ce ba zai iya cewa ga abin da lamarin ke nufi ba, amma ya jaddada muhimmancin samun tsagaita wuta a Gaza.
Read Also:
Shi kuwa firaiministan Qatar, wadda ke shiga tsakani a tattaunawar tsagaita wutar da ake, ya ce mutuwar Mr Haniyeh za ta iya kawo cikas a tattaunawar da ake.
Rasha da China da kuma Turkiyya duk sun yi alawadai da kisan da aka yi masa, inda shugaba Erdogan ya ce an yi hakan ne da nufin karya lagon Falasdinawa.
Wata mata a Tehran ta ce akwai buƙatar mu yi alwadai da wannan ta’addanci da aka yi, sannan ina so Isra’ila ta sani cewa al’ummar mabiya shi’ar Iran ba za su taba bari a kashe musu bako a kasar kuma su yi shiru ba .