Amurka: Mattacen ɗan Takara da Korona ta Kashe ya ci Zaben Majalisa a Kasar
David Andhal, dan takarar jam’iyyar Republican ya rasu sakamakon cutar coronavirus a karshen watan Oktoban 2020.
Jami’an zabe na North Dakota sun ce lokaci ya kure don haka ba za a iya cire sunan Andahl daga takardar kada kuri’a ba.
An sanar da cewa Andahl ya lashe zaben mazabar North Dakota a daren Talata, 3 ga watan Nuwamba bayan samun fiye da 33% na kuri’un da aka kada a zaben Wani dan jam’iyyar Republican da cutar korona ta kashe a watan Oktoba ya yi nasarar lashe zaben majalisa duk da cewa ya mutu.
Read Also:
An sanar da cewa marigayi David Andhal ne ya lashe zaben mazabar North Dakota a daren ranar Talata 3 ga watan Nuwamba bayan ya samu fiye da kashi 35 cikin 100 na kuri’un da aka kada.
Cutar COVID-19 ce ta yi ajalin Andahl. An kwantar da shi a asibiti na makonni kafin daga bisani ya rasu yana da shekaru 55 a duniya.
An zabe shi ne tare da Dave Nehring don wakiltar mazabar da ke zaben wakilai guda biyu.
Mutanen biyu sun samu amincewar ‘yan republican da masu zabe inda suka kada daya daga cikin ‘yan siyasa masu fada aji a North Dakota, Jeff Delzer.
Sakataren gwamnatin jihar Al Jaeger ya shaidawa New York Times cewa jam’iyyar ta Republican wacce ta tsayar da Andahl za ta zabi wani da zai maye gurbinsa.
Ya ce ba kasafai aka fiye samun irin wannan lamarin ba inda ya ce iya saninsa hakan bai taba faruwa ba a shekaru 27 da ya yi yana siyasa.
“A iya sani na, bamu taba samun abu mai kama da wannan ba a baya.”