Amurka ta Sakawa Wasu Takunkumai na Shiga Kasar

Amurka ta kakaba wa wasu kasashen Afrika sabbin takunkumai na shiga kasarta.

A sabuwar dokar tafiye-tafiye na Shugaba Donald Trump, dole sai kasashen sun fara biyan dala 15 kafin amincewa su tafi kasar.

Sabuwar dokar za ta fara aiki ne daga ranar 24 ga watan Disamba.

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sanya wata sabuwar dokar tafiye-tafiye ga kasashen Afrika 15 inda za su biya dala 15,000 kafin su ziyarci kasar.

Wannan sabuwar doka da aka sanya za ta fara aiki ne a ranar 24 ga watan Disamba, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.

A cewar ma’aikatar harkokin wajen kasar, wannan shiri na wa’adin watanni shida wanda zai shafi masu ziyartar Amurka da yan kasuwa zai zamo darasi ga masu zama bayan bizarsu ta kare.

Trump, wanda ya sha kaye a zaben kasar da aka gudanar, ya mayar da tsaurara matakai na shige da fice abu mai matukar muhimmanci a lokacin wa’adin mulkinsa na shekara hudu.

Zababben shugaban Amurka mai jiran gado, Joe Biden ya dau alkawarin sauya wasu matakan da Trump ya dauka musamman kan shige da ficen kasar.

Sabon tsarin bizar zai shafi kasashen da kashi 10 cikin 100 na al’ummansu da ke zuwa Amurka su wuce iya lokacin da aka ba su na zama a shekarar 2019, kuma a yanzu za a nemi su biya wasu kudade kimanin dala 5,000.

da dala 10,000 ko kuma dala 15,000. Sai dai a yayin da yan wadannan kasashe ke wuce lokacin zamansu a Amurka, masu zuwa daga kasashen ba su da yawa, kamar yadda Reuters ya ruwaito.

Kasashen da matakin ya shafa sun hada da: 1. Angola 2. Burkina Faso 3. Chadi 4. Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo 5. Djibouti 6. Eritrea 7. Gambia 8. Guinea-Bissau 9. Liberia 10. Mauritania 11. Sudan 12. Sao Tome 13. Cape Verde 14. Libya 15. Burundi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here