Hajjin Bana: Maniyyata za su Biya N2.8m a Matsayin Kuɗin Kujera

 

Hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya NAHCON, ta sanar da cewa maniyyata aikin hajjin bana za su biya kuɗi da ya kai naira miliyan biyu da dubu 890 a matsayin kuɗin kujera.

Shugaban hukumar Zikrullah Hassan, shi ya bayyan haka a yau Juma’a, inda ya ce matsalar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya da kuma Saudiyya a matsayin abubuwan da suka janyo ƙaruwar kuɗin hajjin bana.

Hassan ya ce farashin ya kai matakai takwas, inda jihohin Borno da Yobe suka kasance jihohi da za su biya kuɗi mafi ƙanƙanta yayin da Legas da Ogun za su biya kuɗi mafi girma da ya kai naira miliyan biyu da dubu 990.

Hakan ya faru ne sakamakon bambancin kuɗin jirgi da kuma kuɗin masaukai a Makka.

Maniyyatan jihohin arewacin ƙasar za su biya naira miliyan biyu da dubu dari tara da goma sha tara.

Jihohin kudancin kasar kuma su ma za su biya kusan miliyan uku.

Hassan ya ce abin da ya sa aka samu bambancin kuɗi shi ne yankin arewacin Najeriya ya fi kusa da Saudiyya a kan kudancin ƙasar, kuma irin masaukin da kowace jiha ke kama wa, shi zai nuna adadin kuɗin da za su biya.

Ya ce kamfanonin jiragen sama da aka amince su yi jigilar maniyyata daga jihohi sun haɗa da Air Peace da Azman da Fly Nas da Aero Contractors da kuma Max Air yayin da Arik Air da Value jet aka amince da su a matsayin jiragen haya masu zaman kansu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here