Ƴan Bindiga sun Kashe Mutane 50 a Jihar Benue

Rahotannin kafafen yaɗa lababru sun ce an gano akalla gawarwakin ƙauyawa 51 da aka kashe a unguwar Umogidi da ke Otukpo a jihar Benue bayan da wasu gungun ‘yan bindiga suka far wa ƙauyen.

An kuma ruwaito cewa ba a ga mutanen kauyen ba da dama kawo yanzu.

Shugaban matasan yankin, Adakole Inalegu Daniel ya shaida wa BBC cewa mazauna yankin, ciki har da kungiyoyin matasa na ci gaba da bincike cikin daji domin gano karin gawarwaki.

Rahotanni sun ce wasu ‘yan bindiga ɗauke da makamai sun mamaye al’ummar yankin a ranar Laraba, inda suka fara shiga ta kasuwar ƙauyen da harbi kan mai uwa da wabi.

Mazauna yankin sun ce da dama daga cikin waɗanda suka kutsa cikin daji, an yi ta harbin su da bindiga, inda aka yanke kawunan wasu daga cikinsu.

Duk da cewa an tura jami’an tsaro zuwa yankin, hakan bai dakatar da waɗannan hare-hare ba.

Mazauna ƙauyukan waɗanda galibi manoma a jihar ta Binuwai, sun sha artabu da makiyaya.

Manoman dai na zargin makiyaya da amfani da dabbobinsu wajen lalata musu amfanin gona, yayin da makiyayan ke zargin manoman da far wa dabbobinsu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here