Jerin Attajiran Duniya: Dangote ya Tashi Daga na 60 Zuwa na 80
Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, ya dawo kasa daga cikin jerin manyan attajiran duniya.
Dangote ya haura zuwa Attajirin Duniya na 60 a watan Yuni kafin ya fado gab da ya shiga jerin attajirai duniya guda 50.
Akwai kadarorin Dangote Masu Daraja da ba saka su a cikin kiddidgar fitar da sunayen attajiran duniya saboda ba su fara aiki ba.
Legas – Aliko Dangote, wanda ya kafa kamfanin Dangote kuma attajirin da ya fi kowa kudi a Nahiyan Afirka, ya ga an daidaita kiyasin dukiyarsa yayin da ake sayar da hannun jari a Simintin Dangote.
Rahoton Legit.NG A lokacin da aka kammala zaman ciniki na ranar Talata, arzikin dan kasuwar dan asalin jihar Kano ya dawo dala biliyan $19, wanda ya mayar da shi 80 a cikin jerin attajiran duniya da kididdigar Bloomberg ta fitar.
Read Also:
A cewar kididdigar Bloomberg, wacce ta fitar da sunayen attajiran duniya 500, yanzu dukiyar sa ta ragu zuwa dala biliyan 19 sabanin dala biliyan 20 a watan Mayun 2022.
Adadin arzikin da Dangote yake da shi a halin yanzu ya sa ya zama mutum na 80 a cikin attajirai a duniya, daga na 60 a cikin watanni biyu kacal da suka wuce.
Farashin da aka yi a kasuwar hada-hadar hannayen jarin Najeriya na baya bayan nan ya nuna cewa Dangote Cement ya rufe kasuwa akan N241.00 a ko wani kaso, inda ya ragu da kashi 9.06 cikin dari, inda ya yi ciniki kusan mako 52 da ya yi kasa da Naira 237, lamarin da ya sa attajirin yayi asarar dala miliyan 863 a kullum.
Mafi akasarin arzikin Dangote ya fito ne daga mallakar kashi 86% na simintin Dangote, wanda ake sayar da shi a bainar jama’a. Kai tsaye da kuma ta hannun kamfaninsa na Dangote Industries, ya mallaki hannun jari a kamfanin kamar yadda nairametrics.com ta rawaito.
Sai dai Kamfanin taki wanda shine mafi daraja a cikin kadarorinsa da matatar mai da ake ginawa a Najeriyana na dala biliyan 19 ba sa cikin dukiyoyin sa da Bloomberg ta sanya a cikin kiddidigar fitar da jerin sunayen attajiran duniya.