Yadda Mahaifi da ‘Dansa Suka Rasa Rayukansu a Cikin Rijiya 

 

Kano- Wani mutum dan shekara 60 mai suna Malam Bala da dansa, Sanusi Bala, ɗan shekara 35 sun mutu a rijiya a Sabon Garin Bauchi, karamar hukumar Wudil na Jihar Kano a lokacin da suke yashe rijiyar.

Mai magana da yawun hukumar kwana kwana na jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya tabbatar da afkuwar lamarin cikin wata sanarwa a ranar Laraba, rahoton Punch.

Sanarwar ta bayyana cewa lamarin ya faru a safiyar ranar Talata.

Abdullahi ya ce:

“Mun samu kiran neman dauki a ofishin mu na Wudil misalin ƙarfe 10.30 na safe daga wani Isma’ila Idris cewa wasu mutane biyu sun makale cikin rijiya. Nan take muka aika tawagar mu na ceto suka isa wurin misalin ƙarfe 11.33 na safe.

“An kira wani mutum da dansa su yashe rijiya. Sun yi nasarar yashe rijiyar. Amma, yaron ya koma cikin rijiyar don kwashe kasar a lokacin ya makale kuma ya mutu saboda rashin iska.

“Mahaifinsa shima ya shiga rijiyar don ya ceto shi yayin da shima ya makale kuma ya rasu saboda rashin iska a cikin rijiyar.”

Sanarwar ta ce an fito da mutanen biyu daga cikin rijiyar a sume kuma daga bisani aka tabbatar sun rasu.

An mika gawarsu ga Sufeta Felix Gowok na ofishin yan sanda na Wudil Model Police Station.

Ya bayyana cewa rashin iskar shaka ne ya yi sanadin mutuwarsu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here