An Tsinci Gawar Mace da Namiji a Cikin Kango Tsirara a Jihar Neja

 

Mutane sun tsinci gawarwakin wasu mutum biyu, namiji da mace tsirara a wani Kango a yankin karamar hukumar Suleja, jihar.

Neja Mutumin da ya fara ganin gawarwakin ya bayyana yadda ya gan su yayin da yaje kusa da Kangon yin bayan gida.

Wannan na zuwa ne yayin da mutane suka fara tashi daga wasu Anguwannin cikin Katsina saboda tsoron yan bindiga.

Niger- An gano gawar Wani mutumi da aka gano sunasa, Adeyemi, da wata mata da ba’a san bayananta ba a wani gini da ba’a karisa ba a Anguwan Gwari, Kwanba a ƙaramar hukumar Suleja, jihar Neja.

Wani mazaunin yankin, Ikechukwu Michael, wanda ya fara ganin gawarwakin ranar Talata, ya bayyana cewa ya je kusa da Kangon da nufin yin bayan gida, sai ya ji wani wari na tsaro wa daga ciki.

Daily Trust ta rahoto a kalamansa Mista Michael ya ce: “Na ga mutumin tsirara babu tufafi a jikinsa yayin da ita kuma budurwan na ganta rabin jiki tsirara.

Tuni fatar gawar marigayi Adeyemi ta fara salewa. Ita macen na ganta kwance kan fuskarta, da ganin haka sai na ankarar da mutane.”

Ya ƙara da cewa jim kaɗan bayan gano gawarwakin mutanen biyu, jami’an yan sanda suka iso wurin, suka kwashe su zuwa ɗakin aje gawarwaki.

Shin yan uwan mamatan basu neme su ba?

Wani wanda ya yi wa marigayi Adeyemi farin sani, Ogundipe Ayo, ya shaida wa wakilin jaridar cewa yayin da ya kira matar mamacin ta nuna masa bata san da faruwar lamarin ba.

A cewarsa, ta shaida masa cewa rabonta da Mai gida tun ranar Lahadi da yamma kuma idan ta neme shi bata samun shi.

Hukumar yan sanda reshen jihar Neja ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba a yanzu da muke kawo muku wannan rahoton.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here