Kwamishinan Gwamna Tambuwal ya Sauya Sheka Zuwa APC

 

Jam’iyyar PDP na ci gaba da ganin tasku a Sokoto yayin da na hannun daman gwamna ya sauya sheka.

Jam’iyyun APC da PDP na ci gaba da kwace mambobi daga rumfunan juna gabanin babban zaben 2023.

A makon nan ne baya ga jihar Sokoto, a Kebbi aka samu yawaitar sauya sheka tsakanin APC da PDP.

Jihar Sokoto – Al’amuran siyasa a jihar Sokoto na kara canzawa gabanin babban zaben badi. Jam’iyyar PDP mai mulkin jihar ta rasa wasu ‘ya’yanta zuwa jam’iyya mai mulkin kasa; APC.

Kanal Garba Moyi (rtd), wanda shi ne kwamishinan ayyuka da harkokin tsaro a gwamnatin Gwamna Aminu Tambuwal ya fice daga PDP ya tsunduma APC, The Nation ta ruwaito.

Ficewar Moyi na zuwa ne jim kadan bayan jam’iyyar ta karbi Kalanjeni da kansilolinsa wadanda su ma suka fice daga PDP zuwa APC a karkashin Sanata Aliyu Wamakko a jihar Sokoto.

Wata sanarwa da mataimaki na musamman kan sabbin kafafen yada labarai na Sanata Wamakko, Bashir Abubakar ne ya fitar da rahoton shigowar Moyi APC.

A cewarsa, Moyi ya fice daga tsohuwar jam’iyyarsa ne saboda rashin amana da mayar da hankali da shugabanci na gari. Moyi ya ce gwamnatin Tambuwal ta karyata alkawarin da ta yi wa al’ummar jihar Sokoto.

Moyi ya ce:

“Na lura da farin ciki ga mutuntaka, tushe da ingantaccen jagoranci na Sanata Wamakko. Wannan ne ya kara min kwarin gwiwa na ficewa daga jam’iyyar PDP, don haka zan iya kasancewa cikin tarihinsa da ba a taba ganin irinsa ba.

“Abin alfahari ne a samu wani irin Sarkin Yamman Sokoto, kuma ya kamata mutane irina su ba su goyon baya domin a samu nasarar gudanar da al’amuran jam’iyyar APC na Sokoto.”

Sanata Wamakko wanda ya tarbi Moyi a gidansa ya bukace shi, kamar sauran mutane, da ya yi aiki tukuru domin kawo nasara ga jam’iyyar, musamman a yankin Sanatan Sokoto ta Gabas da ma jihar baki daya a zaben badi, haka nan Vanguard ta ruwaito.

Wadanda suka halarci liyafar karbar sun hada da dan takarar gwamnan Sokoto, Idris Muhammad Gobir.

Hakazalika da Dan takarar Sanatan Sokoto ta Gabas, Ibrahim Lamido Isa; da takwaransa na majalisar wakilai, Abdulkadir Jelani Danbuga; da kuma shugaban karamar hukumar Sabon Birni, Alhaji Yawale Sarkin Baki.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here