‘Yan Bindiga Sun Shiga Katsina da Tsakar Rana

 

Mutane sun tarwatse yayin da suka ga yan bindiga sun shigo Anguwannin su da tsakar rana a birnin Katsina, jihar shugaban ƙasa.

Wasu da abun ya faru a idon su sun bayyana cewa yan bindigan sun biyo ne yayin da suka taso wasu makiyaya.

Bayanai sun nuna cewa mutane sun fara tattara kayan su suna barin yankin saboda tsoron abinda ka iya zuwa ya dawo.

Katsina – Mazauna Sabon Gida, Anguwar Makudawa, Anguwar Shola Quaters da Asibitin koyarwa na tarayya (FTH) da Anguwar ma’aikatan Katsina sun yi gudun neman tsira yayin da yan bindiga suka shiga yankin da tsakar rana.

A rahoton Daily Trust, wani shaida, wanda ya yi ikirarin ya ga zuwan yan bindigan da karfe 1:30 na rana, ya ce yan ta’addan sun biyo wasu makiyaya ne lokacin da suka shiga Anguwar Sabon Gida.

Shaidan ya ce:

“Makiyayan na tsaka da kiwo a kewayen Lambun Malam Mu’azu, ba zato suka ga yan bindigan, nan take suka fara gudu da dabbobin su zuwa yankin Sabon Gida, hakan ya sa mutane suka fara gudun tsira.”

Wani mazaunin FTH ya ce mafi yawan mutane sun kwashe iyalansu daga yankin sabida tsoron harin yan bindiga, ganin cewa, “Idan yan ta’adda zasu iya zuwa da rana, Allah kaɗai yasan abinda zai faru da daddare.”

Shin dagaske FTH sun ɗauki mataki?

Yayin da aka tuntuɓe shi kan raɗe-raɗin dake yawo cewa an umarci mutane su bar Asibitin FTH, Kakakin Asibitin, Bishir Muhammad, ya ce ba bu wani abu kamar haka daga ofishin Daraktan FTH.

Sai dai ya tabbatar mutane sun shiga tashin hankali a yankin, inda ya ce:

“Mutane sun tsorata, dagaske sun ga yan fashin daji daga nan hankalin su ya tashi kuma idan kaga mutane na tattara kaya zasu tafi, ba zaka hana su ba. Amma maganar gaskiya ba wanda ya umarci su bar yankin.”

Wane mataki hukumomi suka ɗauka?

Mataimakin kwamandan Wakilin Yamma 1, wata ƙungiyar Yan Banga da ke yankin, Abdullahi Usman Ɗan Daura, ya ce duk da barazanar gaskiya ne amma yadda mutane suke zuzuta abun ya ƙara dagula lamarin.

“Muna aiki tare da haɗin guiwar hukumomin tsaro kuma muna iya bakin kokarin mu, amma babban kalubalen na tattare da Imfoma waɗan da ke faɗa wa yan ta’addan mutanen da zasu sace da kuma inda jami’an tsaro suke.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here