Hukumar INEC ta Tsawaita Wa’adin Karɓar Katin Zaɓe

 

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a Najeriya INEC ta tsawaita wa’adin karɓar katin zaɓe da a ke gudanawar a halin yanzu a fadin ƙasar.

A wata sanarwa da kwamishinan hukumar kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da ilimantar da masu kaɗa ƙuri’a Festu Okoye ya fitar ranar Asabar ya ce hukumar ta ƙara wa’adin karɓar katin zaɓen daga 29 ga watan Janairu zuwa biyar ga watan Fabrairu.

Sanarwar ta ƙara da cewa “Hukumar Zaɓe ta zauna a yau Asabar 28 ga watan Janairu kwana guda bayan ta gana da kwamishinoninta na jihohi 36 da Abuja, ta kuma yanke hukunci game da tarin matsalolin da aka gabatar mata , ciki har da batun yadda karɓar katin ke gudana a ƙananan hukumomi 774 na faɗin ƙasar”.

“Sakamakon rahotonnin tsaikon da aka samu na karɓar katin zaɓen da kwamishinonin zaɓen na jihohi suka tattauna hukumar ta yanke hukuncin tsawaita wa’adin karɓar katin zaben zuwa mako guda”.

Wannan dai shi ne karo na biyu da hukumar zaɓen ƙasar ke sauya ranar rufe karɓar katin zaɓen, wanda a baya ta saka ranar 12 ga watan Disamban 2022 kafin ta ɗaga shi zuwa ranar 29 ga watan Janairun da muke ciki.

A ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 ne dai hukumar zaɓen ƙasar za ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasa, da na ‘yan majalisun dokokin ƙasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here