Bayan Bace War sa: An ga Jirgin Yakin Sojojin Saman Najeriya a Borno
An gano jirgin yakin sojojin saman Najeriya da ya bace a yankin arewa maso gabas.
An ga jirgin ne a karamar hukumar Konduga dake da kusanci da garin Maiduguri a Borno.
Amma har a halin yanzu, ba san inda matukan jirgin biyu suke ba ko da aka ga jirgin Alamu sun nuna cewa jirgin yakin sojojin Najeriya da ya bace an gan shi a karamar hukumar Konduga dake jahar Borno mai nisan kilomita 30 daga Maiduguri, babban birnin jahar.
Read Also:
Duk da hukumar rundunar sojin kasan bata riga ta tabbatar da wannan cigaban ba, majiyoyi a ranar Juma’a sun ce an ga jirgin yakin na shawagi a kauyukan Goni Kurmiri da Njimia bayan ragargaza ‘yan ta’adda a Sambisa da yayi.
Majiyoyin sun ce, har yanzu ba a samu labarin inda matukin jirgin da abokin aikinsa suke ba, Channels TV ta wallafa.
Hukumar sojin saman ta sanar da cewa jirgin yakin sojojin ya bace a ranar Laraba da yammaci yayin da yake ayyukan yau da kullum na taimakawa dakarun sojin kasa a yankin arewa maso gabas.
A ranar Juma’a ne rundunar ta sanar da cewa akwai yuwuwar cewa jirgin saman hatsari yayi.
Kamar yadda takardar da rundunar ta fitar daga hannun daraktan hulda da jama’a da yada labarai, Air Commodore Edward Gabkwet, jirgin yana dauke da matuka biyu kuma ya bace a jahar Borno.