Olusegun Obasanjo da Sheikh Gumi Sun Shawarci Gwamnatin Tarayya Kan Matsalar Tsaro

 

Tsohon shugaban kasar Najeriya Obasanjo ya gana da Sheikh Gumi kan batun matsalar tsaro.

Fitattun biyu sun shawarci gwamnatin tarayya da ta kirkiri wasu kotuna don hukunta ‘yan bindiga.

Sun kuma jaddada goyon bayansu ga tallafawa kasar a yaki da take da matsalar rashin tsaro.

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da wani fitaccen malamin addini a Arewa, Sheikh Ahmad Gumi, sun ba da shawarar kafa kotuna na musamman da za su yi shari’ar ’yan bindiga, masu satar mutane da masu safarar muggan makamai a Najeriya.

Obasanjo da Gumi sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka sanya hannu bayan sun yi wata ganawar sirri a dakin karatun Obasanjo dake Abeokuta a ranar Lahadi, jaridar Punch ta ruwaito.

A wani bagnaren sanarwar, ance; “Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta dauki batun da muhimmanci a tsakanin ECOWAS don yin aiki a magance matsalar yankin.

“Kowace al’umma dole ne a karfafa ta kuma a ba ta karfin gwiwa don tsayawa tsayin daka da karfi kan masu laifi.

“Ya kamata a samu kariya da tukuici a boye ga masu tsegunta masu laifi da ke rayuwa a cikin alumma.

“Ya kamata a kirkiro kotuna na musamman don tunkarar shari’ar ‘yan bindiga, satar mutane, neman kudin fansa da kuma daukar makamai ba bisa ka’ida ba.

“Ya kamata taken ya zama:

Tsaro nauyi ne da ke wuyan dukkan ‘yan Najeriya.

“Mun yarda da ci gaba da yin aiki tare don samar da mafita ga tsaron Najeriya da kuma neman wasu su kasance tare da mu kamar yadda muke yada bayanan hadin gwiwarmu a fili”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here