Bayan Sallar Azahar ne aka yi Sallar Jana’izar Sanata Ahmed Mukhtar Aruwa, tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ta kasa.

Sanata Aruwa ya rasu ne da sanyin safiyar ranar Lahadi a wani karamin asibiti a jihar Kaduna.

Mutane da dama ne suka halarci jana’izar Aruwa ciki har da tsohon mataimakin Shugaban kasa Namadi Sambo da tsaffin Gwamnonin jihar Kaduna Ahmad Makarfi da Ramalan Yero da kuma Gwamna mai ci Nasiru el-Rufai.

Cikin wanda suka halarci jana’izar akwai dan takarar Gwamnan Kaduna karkashin inuwar jam’iyyar PDP Isah Ashiru Kudan da kuma dumbin al’ummar Musulmi.

The post An gudanar da jana’izar Sanata Ahmed Aruwa a Kaduna appeared first on Daily Nigerian Hausa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here