An gurfanar da ‘Yan Boko Haram Fiye da 1,000 – Lucky Irabor

 

Rundunar sojojin Nigeria ta ce a kalla yan Boko Haram 500 suna daure a gidan yari

Rundunar ta ce wasu daga cikinsu an yanke musu hukuncin dauri har na shekaru 60

Babban hafson tsaro na Nigeria, Lucky Irabor ne ya sanar da hakan yayin wani taro da aka yi

Lucky Irabor, Babban Hafson Tsaron Nigeria ya ce fiye da yan Boko Haram 500 ne suke tsare a gidan gyaran hali tun bayan kaddamar ta shirin Safe Corridor, rahoton The Cable.

Rundunar Sojin ta kaddamar da Safe Corridor, da nufin sauya tunanin tsofafin yan ta’addan ne tun shekarar 2016.

A cewar sojin, nufin shirin shine mayar da tubabbin yan Boko Haram cikin jama’a. Tsofafin yan Boko Haram fiye da 500 sun kammala shirin.

Da ya ke magana wurin taron da aka yi wa lakabi da “The North-East Symposium on Reintegration, Reconciliation and Resettlement,” a ranar Litinin, Irabor wanda ya samu wakilcin Bamidele Ashafa ya ce an gurfanar da yan ta’adda fiye da 1000.

Ya ce wasu daga cikinsu an musu daurin shekaru 60 a gidan gyaran hali.

“Gwamnatin tarayya bata karfafawa Boko Haram gwiwa. An gurfanar da yan Boko Haram fiye da 1,000. Ina son amfani da wannan damar in sanar da cewa fiye da 500 suna daure a gidan yari cikinsu akwai wadanda za su yi shekaru 60, mafi karancin daurin shine na shekaru 5,” in ji shi.

Mutane da dama sun nuna rashin goyon bayansu da tsarin na sauya tunanin yan ta’addan.

Babagana Zulum, gwamnan Borno ya ce tubabbun yan bindigan sukan zama yan leken asiri su sake komawa kungiyar bayan sauya musu tunanin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here