Bayan Kisan Uwa da Yaranta: Gwamnan Jihar Anambra ya Kafa Dokar Ta-Baci a Kananan Hukumomi 7 na Jihar

 

Gwamna Soludo, a ranar Laraba ya yi jawabi ga al’ummar jihar Anambra tare da kafa dokar ta-baci a kananan hukumomi bakwai na jihar.

A cewar Soludo, dokar ta-bacin za ta fara aiki ne a ranar Juma’a 26 ga Mayu, 2022, a yankuna kamar su Aguata, Ihiala, Ekwusigo, Nnewi ta Arewa, Nnewi ta Kudu, Orumba ta Arewa da Orumba ta Kudu.

Gwamnan jihar Anambra ya kuma yi kira ga mazauna yankunan da abin ya shafa da su hada hannu da gwamnati a wannan umarni.

Jihar Anambra – Wani rahoto da jaridar Daily Trust ta fitar ya ce, gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ya kafa dokar ta-baci fita a kananan hukumomi bakwai na jihar domin daukar mataki kan ayyukan IPOB ke yi.

Yankunan da abin ya shafa sun hada da Aguata, Ihiala, Ekwusigo, Nnewi ta Arewa, Nnewi ta Kudu, Orumba ta Arewa da Orumba ta Kudu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi a jihar a ranar Laraba, 25 ga watan Mayu.

Yadda dokar ta-bacin take

Ya ce dokar ta-bacin za ta fara aiki ne daga ranar Juma’a 26 ga watan Mayu, za ta yi aiki har sai an dawo da zaman lafiya a yankunan da lamarin ya shafa, kamar yadda Punch ta rawaito.

Soludo ya ce:

“Daga gobe Juma’a, 26 ga Mayu, 2022, dokar ta-baci daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe ta ta fara aiki kan babura (okada), keke napep (keke), da motocin bas a Aguata, Ihiala, Ekwusigo, Nnewi ta Arewa, Nnewi ta Kudu, Ogbaru, Kananan Hukumomin Orumba ta Arewa da Orumba ta Kudu har sai an sanar da sabon batu.”

“Har ila yau, an hana babura, keke napep da motocin bas yin aiki a cikin wadannan kananan hukumomin a ranakun Litini har sai lokacin da dokar zaman gida ta tsaya gaba daya.”

Karin bayani na nan tafe..

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here