Mayaƙan Ansaru Sun Hallaka ‘Yan Bindiga 30 a Karamar Hukumar Birnin Gwari
Rahotanni daga Kaduna sun nuna cewa mayaƙan Ansaru sun hallaka yan bindiga aƙalla 30 a karamar hukumar Birnin Gwari.
Bangarorin biyu sun fara gwabzawa da junansu ne tun bayan sharaɗin da Ansaru ta kafa wa yan bindiga.
Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Gwari, Hassan Ibrahim, yace matakan da gwamnatin Kaduna ta ɗauka ya fara haifar da ɗa mai ido.
Kaduna – Rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindiga 30 sun rasa ransu yayin da suka yi arangama da mayaƙan kungiyar Ansaru a jahar Kaduna, kamar yadda Aminiya ta rawaito.
Wasu majiyoyi masu karfi sun nuna cewa ɓangarorin biyu sun fafata da juna ne a kokarin su na nuna karfin iko da yankin ƙaramar hukumar Birnin Gwari.
Hassan Ibrahim, shugaban ƙaramar hukumar Birnin Gwari, ya bayyana cewa rikicin dake faruwa tsakanin waɗannan ɓangarorin biyu ya kawo raguwar satar mutane.
A cewarsa, yanzun yan ta’addan sun fi mayar da hankali kan yadda zasu samu abubuwan more rayuwa kamar fetur da kuɗaɗe.
Read Also:
Matakan gwamnati sun fara haifar da ɗa mai ido Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Gwari yace:
“Ƙungiyoyin biyu na cigaba da arangama da juna suna kashe junansu, kuma hakan yasa an samu sauki sosai wajen garkuwsa da mutane.”
“A halin yanzun yan ta’addan sun fi maida hankali kan samun abubuwan rayuwa kamar fetur da kuɗaɗe. Kwanan nan sun tare wani mutumi a mashin sun kwashe masa man fetur da kuɗaɗe.”
Me ya haddasa faɗa tsakanin ɓangarorin biyu?
Wani mazaunin Zariya kuma ɗan asalin Birnin Gwari yace ɓangarorin biyu sun fara takun saƙa ne bayan ƙungiyar Ansaru ta kafa dokar hana yan bindiga kai hari a yankin.
Fatali da wannan dokar da yan bindiga suka yi shine musabbabin fara faɗa tsakaninsu wanda yakai ga kashe yan bindiga 4 da ɗan Ansaru ɗaya.
Yace tun daga wannan lokaci kuma kowane ɓangare ya fara ƙaddamar da hari ga abokin adawarsa, har takai ga kashe yan bindiga aƙalla 30.
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar yan sandan jahar, Muhammed Jalige, yace ba shi da masaniya, amma zai nemi jin ta bakin DPO na yankin.