Shugaba Buhari ya Bukaci Mambobin APC da su ci gaba da Hada Kansu Sannan su Marawa Sabon Shugabancin Jam’iyyar Baya

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shawarci Sanata Adamu Abdullahi da ya duba cancanta sama da komai wajen zabar yan takara a zaben 2023.

Shugaban kasar ya kuma bukaci mambobin APC da su ci gaba da hada kansu sannan su marawa sabon shugabancin jam’iyyar baya.

Sanata Abdullahi ne ya zama sabon shugaban jam’iyyar mai mulki a taron da aka yi a ranar Asabar, 26 ga watan Maris.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci sabuwar zababbiyar uwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) karkashin jagorancin Sanata Adamu Abdullahi da ta tabbatar da ganin cewa wadanda suka cancanta ne suka mallaki tikitin jam’iyyar a zaben 2023.

Buhari ya bukaci sabbin shugabannin da su inganta damokradiyyar cikin gida da daidaito sannan su tabbatar da ganin cewa ba’a yi cuwa-cuwa ba a zaben fidda gwanin jam’iyyar gabannin zaben 2023, rahoton Punch.

Da yake jawabi a babban taron gangamin jam’iyyar da aka yi a ranar Asabar, a Eagle Square Abuja, shugaban kasar ya kuma yi kira ga mambobin APC da su ci gaba da kasancewa a hade da karfi sannan su marawa sabon shugabancin jam’iyyar baya.

Ya ce:

“Wannan taro na zuwa ne a lokaci mai muhimmanci lokacin da muke shirin wani babban zaben. Don haka, akwai mukatar mu ci gaba da kasancewa cike da kwarin gwiwa da hadin kai domin nasarar jam’iyyarmu.

“Mun yaba da ‘yancin rike ra’ayoyi da buri daban-daban, duk da haka, dole ne kada irin wannan bambance-bambancen ya cutar da Jam’iyyar.

“Ina mai rokonku a kan duk ku ba sabon kwamitin NWC goyon baya domin inganta hadin kai da guje ma wa tunanin da zai iya haifar da rashin jituwa da rashin hadin kai.

“Ga wadanda ke takarar kujerun jam’iyyar, rashin cimma wannan kudiri naku kada ya zama dalilin da zai sa ku juyawa jam’iyyar baya.

“Ya kamata mu dauki dabi’ar yan wasan motsa jiki sannan mu dunga goyon bayan jam’iyyar a koda yaushe domin ta yi nasara.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here