Jam’iyyar APC Zata Ci Gaba da Rajistar mombobi
Jam’iyyar APC ta bayyana ranar da za’a ci gaba da rajistar sababbin mambobi da sabunta tsofaffi.
Jam’iyyar ta shirya tsaf domin gudanar da aiki yadda ya kamata don cimma burin tafiyar 2023.
Hakazalika, gyaran zai shafi dukkan bangarori da matakan jam’iyyar domin bai wa mambobinta haqqoqinsu da suka dace.
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta ce za ta fara rajistar sabbin mambobi tare da sabunta rajista a ranar Litinin, 25 ga watan Janairu, jaridar The Punch ta ruwaito.
Jam’iyyar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da Sakatare mai kula da ita da kuma Babban Kwamitin Shirye-shiryen Taro, John Akpanudoedehe, mai taken, ‘rajistar mambobi, sabuntawa, gwajin sake nuna karfin gwiwa 25 ga Janairu’.
Jam’iyyar a ranar 10 ga watan Disamba, 2020, ta ɗage rajistar mambobinta a duk faɗin ƙasar, sabuntawa, da sake rayarwa da aka shirya tun farko wanda za a fara ranar Asabar, 12 ga Disamba, 2020.
Read Also:
Sanarwar ta karanta, “Mun amince da bukatar ci gaba da sasanta rikice-rikice kuma mun yanke shawarar karfafa sasantawa a dukkan bangarori domin fitowa a matsayin jam’iyya mai karfi, gabanin ‘yan majalisu da babban zaben na 2023.
“Bayan samun amincewar yin rijistar membobin jam’iyyar, yanzu CECPC ta shirya tsaf domin gudanar da aiki yadda ya kamata kuma a cikin wani rubutaccen lokaci, farawa daga 25 ga watan Janairu .
“CECPC an shirya tsaf don gudanar da manyan tarurrukan jam’iyyar a dukkan matakai, ta hanyar adalci da kuma nuna gaskiya wajen zaben jami’ai ga bangarori daban-daban na jam’iyyar da za su kai ga babban taron jam’iyyar na kasa.
“CECPC na aiki don kirkirar tsarin jam’iyya mai cibiya wanda zai tabbatar da cikakken sa hannun dukkan mambobi tare da bayar da dama don karfafa amincewar mambobi, imaninsu, da tsunduma cikin dukkan ayyukan jam’iyyar.
“Ganin cewa lokaci yana son qure mana, CECPC tuni ta ninka kokarinta don saduwa da ayyukan da ke gabanta a shekarar 2021. Dimokiradiyya tana da karfi kamar jam’iyyun siyasar da ta samar; muna sake gina jam’iyyar mu ne domin karfafa demokradiyyar mu. Muna so mu tabbatar wa dukkan mambobinmu cewa sadaukarwar da muka yi don jagorantar aiwatar da sauye-sauyen siyasa a Najeriya ba zai canza ba.”