APC: Dalilin Hukunta Hilliard Eta
Hilliard Eta ya kai karar Jam’iyyar APC kotu a kan tsige Adams Oshiomhole.
Eta ya na kalubalantar matakin da aka dauka na yin waje da majalisar NWC.
Jam’iyyar APC ta ce za ta binciki zargin da ake yi wa Hilliard Eta na yin laifi.
Jam’iyyar APC ta reshen jihar Kuros-Riba ta yanke hukuncin cewa za ta kafa wani kwamiti da zai binciki Hilliard Eta, sannan ya ladabatar da shi.
Ana zargin Mista Hilliard Eta, tsohon shugaban jam’iyyar APC na yankin Kudu maso kudu, da laifin yi wa jam’iyya makarkashiya da zagon-kasa.
Read Also:
Hilliard Eta ya shigar da kara a ranar 26 ga watan Nuwamba, 2020, ta hannun lauyansa, Onyechi Ikpeazu SAN, ya na kalulabalantar tsige su da aka yi.
Eta ya fada wa kotu cewa bai amince da sauke su da aka yi daga kan mukamansu ba.
Eta yana cikin ‘yan majalisar NWC ta Adams Oshiomhole. Lauyan da ya tsaya wa Hilliard Eta, ya roki Alkalin babban kotun tarayya a Abuja da ya kai wa karar, a hana shugabannin rikon kwarya rike jam’iyya.
A dalilin haka jam’iyyar APC a jihar da Hilliard Eta ya fito, ya fitar da jawabi ta bakin shugabanta, Mathew T. Mbu da Ministan wuta, Prince Jedy Agba.
Mai girma karamin Ministan harkar wuta na kasa, Jedy Agba ya na cikin jagororin APC a jihar.