Jam’iyyar APC ta Samu Karin Membobi 6 Daga APGA
Gabanin zaben gwamna na ranar 6 ga watan Nuwamba, a jahar Anambra, jam’iyyar APC ta sake samun karfi.
Wasu ‘yan majalisar jahar shida daga jam’iyyar APGA sun sauya sheka zuwa APC.
Tuni aka gabatar masu da tutar jam’iyyar mai mulki a wani taro da aka yi cikin sirri.
Awka, Anambra – Karfin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben gwamnan Anambra da za a gudanar a ranar 6 ga watan Nuwamba ya samu tagomashi a daren ranar Talata lokacin da ‘yan majalisar dokoki shida karkashin All Progressives Grand Alliance (APGA) suka koma APC.
Shugaban Kwamitin rikon kwarya na APC kuma Gwamnan Jahar Yobe, Mai Mala Buni, ya karbi ‘yan majalisar tare da gabatar masu da tutar APC cikin gaggawa a karshen taron dabarun da aka yi a cikin sirri, jaridar The Nation ta rawaito.
‘Yan majalisan shida su ne: Hon. Nonso Okafor mai wakiltar Nnewi ta Arewa; Hon. Timothy Ifedioramma mai wakiltar Njikoka 1; Hon. Cater D. N Umeoduagu mai wakiltar Aguata 1.
Read Also:
sauran sune Hon. Lawrence Ezeudu mai wakiltar Dumekofia; Hon. Arthur Chiekwu mai wakiltar Idemmih North da Hon. Edward Ibuzo, mai wakiltar Onisha North 2.
Da yake karbar wadanda suka sauya shekar a wani dan takaitaccen biki a yammacin Talata a Abuja, Mai Mala Buni ya sake jaddada kudirin jam’iyyar na lashe zaben gwamnan Anambra, wanda ya sa himma wajen shigar da masu ruwa da tsaki a jahar Anambra.
Buni ya ce:
“Ina kallon abin da ke faruwa, musamman yanzu da fitattun ‘yan majalisar jahar suka fara dawowa jam’iyyar, an samu ci gaba kuma mutanen Anambra suna komawa APC.”
Daga bisani shugaban jam’iyyar ya baiwa ‘yan majalisar tutar APC a karshen wani taron dabarun da aka yi a cikin sirri.
Wadanda suka sauya shekar sun bayyana APC a matsayin wacce aka fi so kuma sun yi alkawarin tattara magoya baya don samun nasara a zaben gwamna na ranar 6 ga Nuwamba.
Da yake nasa jawabin, gwamnan jahar Imo, Hope Uzodinma, ya ce mutanen kudu maso gabas sun farka kuma yankin ya jajirce kan siyasar kasa kuma ya kasance wani bangare na Najeriya. Ya kuma nuna kwarin gwiwa cewa jam’iyyarsa za ta lashe zaben gwamnan jihar Anambra, jaridar Leadership ta rawaito.