Dalilin da Yasa Najeriya ke Fuskantar Matsalolin Tsaro – Gwamna Douye Diri

 

Gwamnan jahar Bayelsa ya bayyana dalilin da yasa Najeriya ke fuskantar matsalolin tsaro.

Ya ce, wasu ‘yan siyasa marasa kima su ke amfani da damar da suke dashi wajen lalata kasa.

A cewarsa, kasar ba wai matsalar tsaro da aka sani kadai fuskanta ba, tana kuma fuskantar matsalar tsaro na siyasa.

Bayelsa – Gwamnan jahar Bayelsa, Mista Douye Diri, a ranar Talata 31 ga watan Agusta ya ce Najeriya ta shiga halin kalubalen tsaro a siyasance ne saboda yawancin ‘yan siyasa suna siyasar son kai don cutar da amfanin al’umma baki daya.

Diri ya kuma ce kasar ta rarrabu fiye da kowane lokaci saboda son kai, kabilanci da rashin kishin kasa da na albarkatun dan adam da na kasa, Punch ta rawaito.

Ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da jawabi a Babban Taron Gudanarwa na Yankin Kudu maso Kudu wanda Cibiyar Gudanarwa ta Najeriya ta shirya a Yenagoa tare da taken, ‘Sarrafa kalubalen tsaro don hadin kan kasa a Najeriya: Matsalar Kudu maso Kudu.’

Diri ya ce baya ga tashin hankali, garkuwa da mutane da sauran kalubalen tsaro, kasar na fama da abin da ya bayyana a matsayin rashin tsaro na siyasa, zamantakewa, kiwon lafiya da abinci.

Gwamnan, wanda ya yi magana ta bakin mataimakinsa, Mista Lawrence Ewhrudjakpo ya nuna cewa matakin rashin tsaro da ke addabar kasar a halin yanzu ba a taba ganin irinsa ba a tarihi.

A cewarsa:

“Rashin tsaro yana zuwa ta hanyoyi daban-daban. Ba wai kawai rashin tsaro bane; hukumomin tsaron mu suna fama da bindiganci, tayar da kayar baya, garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka; muna da rashin tsaro da ke fuskantar tsarin siyasarmu.

“A cikin wannan kasa, muna da yanayin da yawancin ‘yan siyasa ba su da wata kima amma kawai suna biyan bukatun kansu ne.

“Muddin aka kare bukatarsu ko aka biya ta, za su iya barnata duk wani sakamako har ma da muradin mutanen da suke jagoranta. Don haka ne wasu daga cikinsu za su iya canzawa kamar hawainiya da tsallake jirgi cikin sauki.”

Ita ma da take jawabi, Shugabar Cibiyar Gudanarwa ta Najeriya, Misis Patience Anabor, ta lura cewa matakin rashin tsaro na yanzu ya haifar da babbar illa ga tattalin arzikin kasa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here