Kungiyar Arewa ta Tsakiya ta Magantu Kan Kisan da Makiyaya ke wa Yankin

 

Kungiyoyin matasa a yankin arewa ta tsakiya na Najeriya sun ce ba su da wani zabi illa su fara kare kansu daga yanzu.

Yan bindiga sun mamaye yankin inda suke kai farmaki ga garuruwan yankin lokaci-lokaci.

Kungiyoyin sun ce gwamnati ta gaza kare su, saboda haka akwai bukatar su kare kansu daga maharan.

Jos – Wata kungiya mai suna Save Middle Belt Nigeria ta yi Allah wadai da kisan da makiyaya ke yi wa wasu mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a yankin arewa maso tsakiya, inda suka sha alwashin cewa za su fara aikin kare kansu daga yanzu.

Kungiyar ta yi zargin cewa kashe -kashen wani bangare ne na manyan tsare-tsare da makiyayan ke yi don halaka yan asalin yankin da kuma son mallake kasar kakanninsu.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jagoran kungiyar na kasa, Philip Jwan ya sanya wa hannu, kuma jaridar Vanguard ta wallafa.

Kungiyar ta kuma bukaci hukumomin tsaro da su kawo karshen kisan gillar da ‘yan bindigar suke yi wa ‘yan asalin Filato.

Sun kuma yi kira da a gaggauta yin bitar babban tsarin rundunar sojojin kasar don magance rikicin.

Wani ɓangare na jawabin na cewa:

“Daga yanzu, ba za mu ƙara nade hannayenmu muna kallon waɗannan yan ta’addan da yan bindiga suna cimma burinsu na kisan kiyashi ba.

“Kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya ya ba da damar kare kai. Kare kai hakki ne na kundin tsarin mulki.

“Don haka muna neman a gaggauta yin bitar babban rundunar sojojin kasar da kayan aikin leken asiri don magance wadannan munanan lamari da ke barazana ga kafuwar kasarmu.”

Wasu ‘yan Najeriya sun mayar da martani kan matakin matasan arewa ta tsakiya.

Umerie Chibuike Victor ya rubuta a shafin Facebook cewa:

“Ku kashe duk wanda ya zo ya kawo muku hari, wannan gwamnatin ba a shirye take ta magance matsalar rashin tsaro ba. Wannan abun bakin ciki ne.”

Satison Kaura ya rubuta:

“Wannan ita ce hanya mafi kyau ku kare kanku tunda gwamnati ta gaza.

kar ku saurari alkawuran wofi daga gwamnatin Najeriya.”

Ugwuoke Henry ya rubuta:

“Babu sauran mafita ‘yan’uwa. Akwai bukatar ku tashi tsaye ku kare kanku.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here