Corona: Karin Mutane 603 Sun Kamu da Cutar a Najeriya

 

Hukumar daƙile yaɗuwar cutuka ta NCDC a Najeriya ta ce mutum 14 sun rasa rayukansu a ranar Talata sakamakon kamuwa da annobar corona.

NCDC ta ce a yanzu adadin mutane da cutar ta hallaka tun ɓullarta da wannan sabon alkaluma sun kai 2,469, sannan masu dauke da cutar yanzu haka a faɗin ƙasar sun karu daga 10,858 zuwa 11,203.

Jahohin da aka samu wadanda suka sake kamuwa da annobar sun hada da Legas mai mutum 334 da Rivers mai mutum 134.

Akwai Oyo mai mutum 60 da birnin Tarayya Abuja mai mutum 41 da Osun 20 da kuma Filato 14.

Sauran jahohin irinsu Ogun 9, da Ekiti 7, da Kwara 6, da Benue mutum 1.

NCDC ta ce mutum miliyan 2.7 aka yiwa gwajin cutar a faɗin ƙasar sai dai cikin wannan adadi mutum 192,431 ne aka samu dauke da cutar tun bullarta a watan Fabarairun 2020.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here