2023: Jamiyyar APC na Samun Karuwar Mambobi Daga Jam’iyyar PDP

Ana ta samun sauye-sauye a sararin siyasar Najeriya gabanin babban zaben na 2023.

Ya zuwa yanzu, da alama jam’iyyar adawa ta PDP tana shan kaye inda yawancin jiga-jiganta suke sauya sheka zuwa APC.

Karin mambobin jam’iyyar adawar sun koma jam’iyya mai mulki a Ribas a ranar Laraba, 21 ga watan Yuli.

Jam’iyyar Peoples Democratic Party a jahar Ribas ta rasa manyan jiga-jiganta guda hudu a hannun jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a ranar Laraba, 21 ga watan Yuli.

Masu sauya shekar, wadanda suka fito daga karamar hukumar Khana ta jahar sune Dumka Philip Rojas, tsohon shugaban majalisar dokokin Khana, Lekia Nwanikpo, tsohuwar mai kula da ayyuka na musamman, Dumbete Obegu, da kuma tsohon mashawarci na musamman ga shugaban majalisar Khana, Dum Ntorue, Leadership ta ruwaito.

A madadin Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, wani jigo jam’iyyar APC na Ribas, Injiniya Chukwudi Dimkpa, ya karbi sabbin mambobin tare da yaba musu kan jajircewarsu, inda ya kara da cewa dukkansu za su more dama daidai da kowa kuma za a dama da su a jam’iyyar.

Rojas ya yi ikirarin cewa shi da sauran wadanda suka sauya sheka sun fice daga PDP ne saboda zargin nuna kiyayya ga gwamnatin jahar.

Ya ci gaba da bayyana cewa APC ta zama abin sha’awa a gare su saboda dimbin ayyukan ci gaba da nade-naden mukaman tarayya da aka ba jahar sakamakon kyakkyawan ayyukan ofishin Amaechi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here