2023: Ina Fatan APC Zata yi Koyi da Abinda Jam’iyyar PDP ta yi a 2015 – Nyesom Wike
Nyesom Wike, gwamnan jihar Ribas, ya ce ‘yan Nigeria sun kosa shekarar 2023 ta zo domin PDP ta koma mulkin kasa.
Gwamna Wike ya bukaci jam’iyyar APC ta yi koyi da abin da PDP ta yi a shekarar 2015 na mika mulki bayan faduwa zabe.
Wike ya gargadi jam’iyyar APC akan kar ta kuskura ta yi yunkurin sauya zabin ‘yan Nigeria a shekarar 2023.
Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bukaci jam’iyyar APC mai mulki ta fara tsara wasiyya gabanin karewar wa’adin mulkinta a shekarar 2023, kamar yadda The Nation ta wallafa.
Wike ya cika bakin cewa ‘yan Nigeria sun kagu 2023 ta zo domin jam’iyyar PDP ta karbi mulki a kasa domin cigaba da shugabanci mai ma’ana.
Read Also:
Gwamnan na jihar Ribas ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da jawabi a wurin bikin kaddamar da wata hanya mai nisan kilomita 11.53 a karamar hukumar Oyigbo.
A wani jawabi mai dauke da sa hannun mai taimaka masa a bangaren yada labarai, Wike ya ce PDP ta na yin ayyukan da ‘yan kasa ke bukata a dukkan jahohin da take mulki.
Kazalika, ya bayyana cewa hakan shine salon shugabancin jam’iyyar PDP a lokacin da take mulkin kasa.
Wike ya bukaci babban bakonsa, Sanata Ndume, da jam’iyyar APC da su mutunta zabin ‘yan Nigeria, wadanda ikon dawo sa PDP mulki ke hannunsu.
A karshe, Wike ya ce yana fatan APC zata yi koyi da abinda jam’iyyar PDP ta yi a 2015, ta mika mulki cikin ruwan sanyi idan ta sha kaye wurin ‘yan Nigeria a 2023.
A ranar Lahadi, 3 ga watan Janairu, ne Legit.ng ta rawaito cewa fadar shugaban kasa ta yi raddi tare da yi wa jam’iyyar adawa ta PDP kaca-kaca.
A cewar fafa shugaban kasa, jam’iyyar PDP ba ta yi komai ba a tsawon mulkinta na shekaru goma sha shidda bayan assasa cin hanci da rashawa.