APC na da Mabiya Miliyan 40 a Najeriya- Sanata Akpanudoedehe

John Akpanudoedehe yace jam’iyyar APC tana da mabiya miliyan 40 a Najeriya.

Sanata Akpanudoedehe yake cewa wannan ne zai ba APC damar lashe zaben 2023.

Sakataren na APC ya sha alawashi yin nasara a zabukan Ekiti, Osun da Anambra.

Abuja – Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) tace za ta yi galaba da kyau a zabukan gwamnonin jahohin da za ayi a Anambra, Osun da Ekiti.

Jaridar Premium Times ra rahoto sakataren jam’iyyar APC na rikon kwarya, Sanata John Akpanudoedehe yana cewa suna da mabiya miliyan 40.

John Akpanudoedehe ya bayyana wannan ne a lokacin da yake kadammar da kwamitocin da za su saurari korafai a zabukan da APC ta gudanar a jahohi.

An rahoto Akpanudoedehe yana cewa a cikin sauki jam’iyyar APC za ta lashe zabe, saboda adadin mabiyanta.

Sakataren jam’iyyar na riko yake cewa akwai kokarin da APC ta ke yi na ganin ta kara karfi, sannan ta kafa gwamnatoci a Anambra, Osun da Ekiti.

Mutum miliyan 40 suka yi rajista da APC – Akpanudoedehe “Da adadin dinbin mabiyanmu da suka yi rajista, babu shakka mutanen Najeriya sun yadda da mu, kuma za mu lashe zabukan da za a yi.” – Akpanudoedehe.

“Fara wa da zabukan Anambra, zuwa Osun, da Ekiti dakuma babban zaben zaben 2023.”

Akpanudoedehe yace al’umma sun fahimci Muhammadu Buhari yana da niyyar alheri, kuma zai yi bakin kokarinsa wajen samar da abubuwan more rayuwa.

Sakataren na APC yace dole a hada-kai domin yakar wadanda suka sha alwashin ruguza kasa, ya kawo misali da kai hari a filin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

A karshe, Akoanudoedehe ya yi kira ga ‘yan kwamitin da aka kafa da su yi adalci, su saurari korafi daga kowane bangare yayin da ake fama da rigingimu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here