Jam’iyyar APC za ta Zama Mafi Girman Jam’iyya a Nahiyar Afirka – Gwamnan Kogi
Gwamna Yahaya Bello na jahar Kogi ya ce kwanan nan jam’iyyar APC za ta zama shahararriyar jam’iyya a nahiyar Afirka.
A cewar gwamnan, za su koyar da har shugabannin wasu kasashe makaman da za su bi idan suna son samun nasara a zabe.
Ya kara da cewa, sai APC ta zama tamkar wata jami’a ta koyar da siyasa, wacce mutane da dama za su yi dubi da ita.
Gwamnan jahar Kogi, Yahaya Bello, ya ce kwanan nan jam’iyyar APC za ta zama mafi girman jam’iyya a nahiyar Afirka, The Cable ta wallafa.
Ya yi maganar ne a ranar Talata, lokacin da ake rijistar sababbin ‘yan jam’iyya da kuma tabbatar da tsofaffin ‘yan jam’iyyar, inda yace har wasu kasashe masu cigaba za su bukaci neman sani akan siyasa daga APC.
Read Also:
Ya kamata a yi taron ‘yan jam’iyyar a ranar 12 ga watan Disamban 2020, amma sai aka daga zuwa mako na biyu na watan Janairun 2021.
Gwamnan jahar Kogi ya ce zai yi aiki tukuru wurin ganin jam’iyyar APC ta samu nasarori a zabukan da za a yi a kasar nan.
“Ba zama muka yi ba da ake ganin duk zaben da za a yi a jahar Kogi sai mun samu nasara. Da izinin Ubangiji, za mu yi hakan a zabukan gaba daya kasarnan,” a cewarsa.
“Lokacin da muka gama duk wasu rijistar ‘yan jam’iyya da kara tabbatar da tsofaffin ‘yan jam’iyya a kasar nan, APC sai ta zama jam’iyyar da tafi ko wacce shahara a nahiyar Afirka, kuma sauran kasashe za su zo sanin makamar siyasa daga APC.
“Zamu koya wa ‘yan uwan mu yadda ake samun nasara a zabe. Ba zan kira sunaye ba, amma zamu zama tamkar jami’a ta koyarwa akan harkar siyasa a Najeriya,” ya kara da cewa.