Jam’iyyar APC ta Kasa ta yi Martani Kan Dakatar da Rotimi Amaechi
Hedkwatan jam’iyyar APC ta kasa ta soke dakatarwa da wani tsagin jam’iyyar a Jihar Rivers ta yi wa Rotimi Amaechi.
Uwar jam’iyyar ta ce wadanda suka yi dakatarwar ba su ne halastattun shugabannin jam’iyyar a jihar ba don haka ba su da ikon dakatar da wani.
Har wa yau, uwar jam’iyyar ta gargadi tsagin Igo Aguma cewa zata dauki matakin ladabtarwa a kansu muddin ba su dena ikirarin sune shugabanni ba.
Kwamitin rikon kwarya na na kasa na jam’iyyar APC karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni, a ranar Laraba, ta soke dakatarwar da aka ce an yi wa Ministan Sufuri, Rotimi Ameachi da wasu mambobin APC a Jihar Rivers, The Punch ta ruwaito.
Tsagin jam’iyyar APC masu yi wa Igo Aguma biyayya a Rivers ta sanar da dakatar da Ameachi, Sanata Andrew Uchendu da tsohon mataimakin sakataren APC na kasa, Victor Giadom kan zargin cin amanar jam’iyyar.
Read Also:
Uwar jam’iyyar ta aike da wasika ga jam’iyyar reshen Jihar Rivers game da dakatar da su Ameachi ga Igo Aguma inda ta gargadi tsaginsa ta dena aikata wani abu da zai iya kawo tashin hankali a jam’iyyar.
Shugabannin jam’iyyar na kasa sun ce suna bukatar lokaci don yin bincike kan jan hankalinsu cewa akwai wasu da ke ikirarin su shugabanin jam’iyyar ne a matakin mazabu.
Wani sashi na wasikar ya ce, “Mun duba sunayen da muka da shi na shugabannin jam’iyyar a sakatariya kuma mun gano wadannan mutanen ba sune shugabannin jam’iyya a Rivers ba.
“Don haka, an shugaban jam’iyya, Mai girma, Gwamna Mai Mala Buni, ya umurce ni in sanar da kai cewa Hon. Isaac Ogbobula ne shugaban APC na Jihar Rivers da aka rantsar a sakatariyar kasa da Disamban 2020 yayin taron shugabannin jam’iyya da aka yi a Aso Rock, Abuja.”
Wasikar ta kara da cewa, “Ina son janyo hankalinka da sauran mambobin APC na Jihar Rivers game da hukuncin da kundin tsarin mulkin jam’iyya da na kasa suka tanada ga masu yin sojan gona.”