2023: Jam’iyyar APC ta Sanar da Ranar Fara Gudanar da Kamfen Dinta na Shugaban Kasa

 

Jam’iyyar APC ta sanar da cewa za ta fara gudanar da harkokin kamfen dinta na shugaban kasa na 2023 a ranar Litinin, 10 ga watan Oktoba.

Jam’iyyar mai mulki ta sanar da hakan ne duk da cewar dan takararta na shugaban kasa, Bola Tinubu, yana chan a birnin Landan.

Ana sanya ran tsohon gwamnan na jihar Lagas zai dawo kasar a cikin wannan makon.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa jam’iyyar All Progressives Congress APC za ta kaddamar da yakin neman zabenta na shugaban kasa na 2023 a ranar Litinin, 10 ga watan Oktoba.

Hakan na zuwa ne yayin da jam’iyyar da kwamitin kamfen dinta ke shirin tarbar dan takararsu na shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, wanda ya tafi kasar Ingila.

Jaridar ta rahoto cewa ana sanya ran Tinubu wanda ya shafe yan kwanaki a birnin Landan zai dawo gida Najeriya a cikin wannan makon.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here