Jam’iyyar APC ta Rushe Kwamitin Neman Zaɓen Shugaban ƙasa na 2023
Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta rushe kwamitin da ta kafa a bara na yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, wadda ta samu sa-hannun babban daraktan kwamitin Simon Bako Lalong da kuma sakataren kwamitin James Abiodun Falake.
Jam’iyyar ta yi godiya a madadin shugaban yaƙin neman zaɓen 2023 Muhammadu Buhari, ga duka mutanen da suka taimaka aka kai ga nasarar da aka samu.
Read Also:
“Tun lokacin da aka fara yaƙin neman zaɓen a watan Satumbar 2022, mun ga yadda lamura suka rika tafiya ba daidai ba a wannan lokacin, kuma mun ga waɗanda suka yi mana daɗi, har muka kai ga nasara”, kamar yadda sanarawar ta bayyana.
Jam’iyyar APCn ce dai ta samu nasara a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
Inda ɗan takararta Bola Ahmed Tinubu ya samu rinjaye da ƙuri’u miliyan 8,794,72.
A ranar 29 ga watan Mayu ne kuma za a rantsar da shi a matsayin sabon shugaban Najeriya