2023: Farin Jini Jam’iyyar APC na Iya Samun Tangarda a Lokacin da Shugaba Buhari Zai Bar Mulki – Osinbajo
Tuni jam’iyya mai mulki, All Progressives Congress, ke shirin yadda za ta ci gaba da kasancewa mai tasiri bayan wa’adin mulkin Shugaba Buhari.
Mataimakin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo, ya fadawa membobin jam’iyyar abin da ya kamata a yi don samun nasarar jam’iyyar a gaba.
Babbar jam’iyyar adawa, Peoples Democratic Party, ta riga ta yi alkawarin kayar da APC a babban zaben 2023.
Abuja – Mataimakin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo, ya ba da shawarar cewa farin jinin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na iya samun tangarda a lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya bar mulki.
Read Also:
Osinbajo a ranar Litinin, 16 ga watan Agusta, ya shaidawa mambobin kungiyar matasa na jam’iyyar APC na kasa cewa yayin da jam’iyyar ke samun farin jini a halin yanzu a karkashin jagorancin shugaban kasa, lamarin na iya sauyawa bayan mulkin Buhari a 2023.
Kamar yadda jaridar This Day ta ruwaito, ya bukaci matasan jam’iyyar da su hada kan matasan Najeriya a fadin kasar don shiga jam’iyyar tun daga matakin unguwa.
Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa dole ne membobin jam’iyyar su yi aiki tukuru don jawo kuri’u zuwa APC.
Osinbajo ya ce:
“A yau, APC za ta iya cin zabe, me zai hana, muna da Shugaban kasa mai farin jini wanda zai iya sarrafa manyan kuri’u, muna da abokan hulda a ko’ina.
“Alhalin, a cikin shekaru masu zuwa, lokacin da ba mu da irin wannan jagoran siyasa wanda ya shahara kamar Shugaban ƙasa, za ka buƙaci yin aiki tukuru. Ba za mu iya ɗaukar cewa duk ƙuri’un za su shigo ba.”
Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, ya bayyana kwarin gwiwarsa kan karfin matasan na iya yin abubuwa a dukkan bangarorin siyasa.