Jam’iyyar APC ta Sanar da Ranar Fara Rijista
Jam’iyyar APC mai mulki ta sanar da cewa ta tsayar da ranar 12 ga watan Disamba domin fara rijistar sabbi da sabunta rijistar tsofin mambobinta.
Mai Mala Buni, shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC, ya bukaci tsofin mambobi su sabunta rijistarsu a mazabunsu.
Buni, gwamnan jihar Yobe, za su cigaba da fitar da sanarwa akai akai dangane da rijistar mambobin APC.
Kwamitin kula da tsare – tsare na jam’iyya mai mulki, APC, sun ce sun kammala duk shirye-shirye don fara aiwatar da sabuwar rijista da sabunta rijistar ƴan jam’iyya daga ranar 12 ga watan Disamba.
Read Also:
Shugaban kwamitin, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ne ya fadi hakan a sanarwar da suka fitar a birnin tarayya, Abuja, ranar Litinin bayan ganawa da masu ruwa da tsaki, wanda suka haɗa da Shugaba Muhammad Buhari.
Ya ce za’a fara rijistar shaidar zama ɗan jam’iyya daga ranar Asabar, 12 ga Disamba, 2020 zuwa Asabar, 9 ga watan Junairu, 2021.
“Mu na gayyatar dukkan ƴan jam’iyyarmu da su sabunta shaidarsu a mazaɓunsu.
“Haka zalika muna kira da ƴan jam’iyya da basu da rijista da suyi amfani da wannan damar don zama cikakkun ƴan jam’iyyarmu.
“Za’a gudanar da rijistar a dukkan mazaɓun ƙasar nan. Za’a kammala kai kayan rijista da sauran kayayyakin aiki zuwa kowacce jiha da ƙananan hukumomi kafin ranar 12 ga watan Disamba, 2020.
“Mu na kira ga Shugabannin jihohi, ƙananan hukumomi da mazaɓu su ɗauki dukkan matakan da suka dace don tabbatar cewa al’amurra sun tafi cikin tsari da daidaito yayin gudanar da rijistar.
“Za mu cigaba da bada bayanai akai akai” a cewar gwamna Buni.