Gombe: Jam’iyyar PDP na Zargin APC da Shirya Murɗe Sakamakon Zaɓen Jihar
Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta tono wani shirin jam’iyyar APC na murɗe zaɓe a jihar Gombe.
Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa tana da sahihiyar hujja a hannun ta inda gwamnan jihar ya kitsa yadda za a murɗe zaɓen jihar.
Sai dai jam’iyyar APC a jihar ta musanta waɗannan zarge-zarge inda ta bayyana cewa a matsayin tsantsagwaron ƙarya.
Jihar Gombe- Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Gombe, ta zargi gwamnan jihar, Inuwa Yahaya, da shirya yadda za a murɗe sakamakon zaɓen dake tafe a jihar.
Kakakin jam’iyyar PDP na jihar, Ayuba Aluke, shine yayi wannan zargin a yayin ganawa da ƴan jarida ranar Talata, inda yace gwamnan ya gama shirin yin maguɗi a zaɓen. Rahoton The Cable.
Read Also:
Aluke ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ta samu wata hujja ta sautin murya na yadda za a murɗe zaɓen, sannan tuni har ta miƙa ta ga hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) da jami’an tsaro domin ɗaukar matakin da ya dace.
Yayi Allah wadai da hanyoyin da APC ke bi na ko ta halin ƙaƙa sai ta cinye zaɓe a jihar, ta hanyar siyan ƙuri’u, yin barazana da lalata na’urar tantance masu kaɗa ƙuri’a (BVAS) domin samun sakamakon da suke so.
“Mun yi sa’ar samun wasu bayanai da wasu muhimman bayanan sirri.” Inji shi
“Muna da sahihin sautin murya inda gwamna mai ci yanzu na inuwar jam’iyyar APC, yake tattaunawa da bayar da bayanai ga wasu gungun na kusa dashi.”
“Ya bayyana cewa yana shirin yin maguɗi da murɗe zaɓen da kuma yiwa na’urar BVAS wayau da sauran dokokin zaɓe na. ƙasa.”
Jam’iyyar APC ta musanta zargin
Da yake mayar da martani kan zargin nasa, Ismaila Uba-Misilli, kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC a jihar, jam’iyyar ta firgita ne kawai da nasarorin da Inuwa Yahaya ya samu. Rahoton NAN
Uba-Misilli yace mambobin jam’iyyar PDP sun koma ƴaɗa ƙarerayi ne kawai saboda suna da masaniyar cewa kashi za su sha a ranar zaɓe.