Kwamitin Zartarwa na Jam’iyyar APC Reshen Jahar Enugu Sun Tsige Shugaban Jam’iyyar

 

‘Yan kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC a jahar Enugu sun kaɗa kuri’ar tsige shugaban APC na jahar.

Kwamitin ya zargi tsohon shugaban da nuna rashin ɗa’a da kuma fatali da dokokin APC wajen gudanar da gangami.

Kwamitin mai mambobi 42 ya amince da naɗin mataimakinsa a matsayin shugaban riko na APC a jahar.

Enugu – Mambobin kwamitin zartarwa (SEC) na jam’iyyar APC reshen jahar Enugu sun tsige shugaban jam’iyyar, Dr. Ben Nwoye, daga mukaminsa Leadership ta rahoto cewa mambobin sun ɗauki wannan matakin ne bisa zarginsa da kokarin tarwatsa jam’iyyar APC a jahar.

Daga nan ne suka naɗa mataimakin shugaban, Prince Chikwado Chukwunta Nnaji, a matsayin shugaban APC a Enugu na rikon kwarya.

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da kwamitin mai mambobi 42 ya fitar ɗauke da sanya hannunsu ranar Talata.
Wane dalili yasa aka tsige shugaban?

Kwamitin zartarwa ya zargi tsohon shugaban da nuna halin rashin ɗa’a da yin fatali da shinfiɗaɗɗen tsarin gudanar da gangamin taron APC wanda kwamitin rikon kwaryar APC ta kasa ya samar.

Hakanan kwamitin ya zargi tsohon shugaban da ƙin yin amfani da kundin tsarin mulkin APC wajen jagorancinsa, kamar yadda PM News ta ruwaito.

Da yake jawabi ga manema labarai, shugaban rikon kwarya, Prince Gilbert C. Chukwunta, yace:

“Mambobin kwamiti sun haɗu domin ceto jam’iyyar mu daga rugujewa matukar Nwoye ya cigaba da jagorancin jam’iyyar APC a jahar.”

Waɗanda suke tare da shi yayin wannan jawabin sun haɗa da sakatare, Chief Robert Eze, da shugabar mata, Hon Mrs Oby Nwofor.

Sauran sun haɗa da shugaban matasan APC na jahar, Joshua Mamah, da kuma sakataren kuɗi, Dr. Mrs. Amaka Adonu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here