Nasarawa: Muna da Yaƙinin Lashe Zaɓukan Kananan Hukumomin jahar – APC
Kakakin majalisar dokokin jahar Nasarawa, Ibrahim Abdullahi, ya bayyana cewa babu tantama APC zata lashe zaɓukan kananan hukumomin jahar.
A cewarsa waɗanda suke jagorantar PDP a baya sun sauya sheka zuwa APC, sabida haka APC zata samu nasara baki ɗaya.
Gwamna Abdullahi Sule na jahar Nasarawa, ya yi kira ga mambobin APC su fara yakin neman zaɓe gida-gida domin jawo hankalin jama’a.
Nasarawa – Kakakin majalisar dokokin jahar Nasarawa, Alhaji Ibrahim Abdullahi, ya bayyana yaƙininsa cewa jam’iyyar APC zata lashe zaɓen kananan hukumomin jahar, wanda za’a gudanar ranar 6 ga watan Oktoba.
Abdullahi ya faɗi haka ne a wurin taron kaddamar da yaƙin neman zaɓen APC a Toto, hedkwatar ƙaramar hukumar Toto, ranar Laraba, kamar yadda Vanguard ta rawaito.
Read Also:
Yace ƙaramar hukumar Toto na ɗaya daga cikin yankunan da APC take da karfi, ya kuma tabbatar da cewa APC ce zata lashe zaɓen ciyaman da na kansiloli.
Yace:
“Babu wata jam’iyya kamar APC, karamar hukumar Toto zata cigaba da kasancewa tamkar gidan jam’iyyar APC.”
“Masu rike da PDP a baya, yanzun sun dawo jam’iyyar APC. Saboda haka APC zata samu nasara a zaɓen 6 ga watan Oktoba.”
“Ranka ya ɗaɗe, inason tabbatar maka da cewa ba zamu baka kunya ba a ƙaramar hukumar Toto, zamu samu nasara a zaɓe mai zuwa.”
Ku shiga gida-gida neman ƙuri’u – Gwamna Sule
Gwamna Abdullahi Sule, ya roki masoyan jam’iyyar APC su fara yaƙin neman zaɓe gida-gida domin jawo hankalin mutane su zaɓi APC.
Sule, wanda mataimakinsa, Emmanuel Akabe, ya wakilta, ya yabawa kakakin majalisa da sauran jiga-jigan jam’iyya na yankin bisa sadaukarwarsu wajen goyon bayan APC.