Kundin Tsarin Mulkin Jam’iyyar APC ya Bada Zabi Uku na Yadda za’a Gudanar da Zaben Fidda Gwani
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi watsi da tsarin kato bayan kato wajen zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na zaben 2023 sabanin yadda tayi a zaben 2019.
Jam’iyyar ta yanke shawarar amfani da deleget wajen zaben wanda zai wakilci jam’iyyar a zaben shugaban kasa.
An yanke shawarar haka ne a taron Majalisar zartaswa NEC ta 11 da ya gudana a Transcorp Hotel a watan Afrilu a birnin tarayya Abuja.
Kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC ya bada zabi uku na yadda za’a gudanar da zaben fidda gwani.
Ittifaki, yar tinke wanda aka fi sani da kato bayan kato, da kuma na deleget.
Jam’iyyar APC na da Deleget 7,800.
Read Also:
Yayinda jihar Kano tafi yawan deleget, Abuja ke da mafi karanci.
Legit ta tattaro muku adadin deleget da kowace jiha ke da shi:
Kano: 465
Katsina: 384
Borno:324
Osun: 308
Lagos: 304
Oyo: 292
Jigawa: 266
Niger: 251
Ogun: 248
Nasarawa: 245
Abia: 154
Adamawa: 184
Akwa Ibom: 165
Anambra: 163
Bauchi: 202
Bayelsa: 79
Benue: 180
Cross River: 194
Delta: 170
Ebonyi: 154
Edo: 168
Ekiti: 216
Enugu: 131
Gombe: 134
Imo: 236
Kaduna: 234
Kebbi 213
Kogi: 222
Kwara: 195
Ondo: 200
Plateau: 185
Rivers: 151
Sokoto: 193
Taraba: 146
Yobe: 222
Zamfara: 169
FCT: 53