Sakamakon Zaɓe: Jam’iyyar APC ta Lashe Zaɓen kananan hukumomi 8 a Jahar Kaduna
Bayan kammala zaben kananan hukumomi a jahar Kaduna, sakamako ya fara fitowa daga bakin baturen zabe.
Rahoto ya nuna cewa an gudanar da zaɓe a kananan hukumomi 19 cikin 23 dake jahar.
A halin yanzun, jam’iyyar All Progressive Congress (APC) mai mulki ta lashe 8 yayin da PDP ta samu ɗaya tal.
Kaduna – Sakamakon zaɓen kananan hukumomi da aka gudanar ranar Asabar a jahar Kaduna ya fara hitowa, kamar yadda dailytrust ta rawaito.
Legit.ng Hausa ta gano cewa an gudanar da zaɓen a kananan hukumomi 19 cikin 23 dake jahar Kaduna.
Daga cikin kananan hukumomi 9 da aka bayyana sakamakonsu zuwa yanzun, APC ta lashe 8 yayin da babbar abokiyar hamayyarta PDP ta samu ɗaya.
Ga yadda sakamakon yake fitowa:
Karamar hukumar Kubau
Baturen zaɓen karamar hukumar Kubau, Mallam Dayyabu Muhammed, ya sanar da Bashir Zuntu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Baturen zaɓen yace ɗan takarar na APC ya samu kuri’u 23,973, wanda ya bashi damar Lallasa abokan takararsa na PDP, Malam Isa Rabiu Imam, mai kuri’u 9,038.
Kudan
Mista Haruna Abdu, baturen zaɓen karamar hukumar Kudan, ya bayyana Alhaji Shu’aibu Jaja, na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓe da kuri’u 18,129.
Jaja ya samu nasarar doke Ibrahim Shehu Doka, na jam’iyyar PDP, wanda ya samu kuri’u 16,123 da Umar Taba na Labour Party, wanda ya samu kuri’u 1,844.
Lere
Read Also:
A karamar hukumar Lere, Alhaji Abubakar Buba, na jam’iyyar APC, shine ya samu nasara da kuri’u 36,389, inda ya doke Dalhat Abu-Dadda’i na jam’iyyar PDP, wanda ya samu kuri’u 24,294.
Zaria
Hakazalika, Alhaji Idris Ibrahim, na jam’iyyar APC ya lashe kujerar shugaban ƙaramar hukumar Zaria da kuri’u 34,006.
Inda ya lallasa babban abokin takararsa na jam’iyyar PDP, Alhaji Yusuf Sambo, wanda ya samu kuri’u 14,019 dai-dai.
Sabon Gari
Alhaji Mohammed Usman, na jam’iyyar APC shine ya lashe zaɓen karamar hukumar Sabon Gari da kuri’u 32,405, ya doke Alhaji Abdu Bello na PDP mai kuri’u 13,777.
Jema’a
Yunana Markus Barde na jam’iyyar APC ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙaramar hukumar Jema’a da kuri’u 24,255.
Wannan nasarar ta sa APC ta doke shugaban da ya gabata na jam’iyyar PDP, Peter Danjuma Averik, wanda ya sami kuri’u 23,215.
Baturen zaɓen Sanga, Dakta Sunday Ibrahim, shine ya sanar da sakamakon bayan kammala tattarawa.
Kaura
Baturen zaɓen Kaura, Farfesa Katoh Ishaya, ya sanar da ɗan takarar PDP, Matthias Siman, a matsayin wanda ya lashe zaɓen ƙaramar hukumar da kuri’u 19,511.
Siman ya lallasa babban abokin takararsa na jam’iyyar APC, Adamu Donatus, wanda ya samu kuri’u 10,941.
Sanga
Da yake sanar da sakamakon zaɓen, baturen zaben karamar hukumar yace ɗan takarar APC, Bisallah Malam, ya samu kuri’u 21,854, inda ya samu nasara a kan abokin takararsa na PDP da ya samu kuri’u 12,832.
Kagarko
Baturen zaɓe, Dakta Musa Balarabe Makarfi, ya bayyana ɗan takarar APC, Hon. Nasara Rabo, a matsayin wanda ya lashe zaɓen karamar hukumar Kagarko da kuri’u 20,558.
Rabo ya doke abokin takararsa na jam’iyyar PDP, Caleb Pius, wanda ya samu kuri’u 14,494.