APC: Abinda ya Taimaki Jam’iyyar a Zabukan 2015 da 2019

 

Fasto Tunde Bakare ya yabi Jagoran jam’iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu.

‘Dan siyasar ya ce Bola Tinubu ya taimaka sosai wajen samun nasarar APC.

Ya ce ba don Tinubu ba, da APC ba za ta iya lashe zabukan 2015 da 2019.

Shugaban cocin Citadel Global Community Church, wanda aka sani a baya da Latter Rain Assembly, Tunde Bakare, ya yabi Asiwaju Bola Tinubu.

A ranar Laraba, 23 ga watan Disamba, 2020, aka ji Fasto Tunde Bakare ya na yabon tsohon gwamnan na Legas kuma babban jagoran jam’iyyar APC.

Malamin addinin ya bayyana cewa Ubangiji ya riga ya yi wa Asiwaju Bola Tinubu daukaka, ya ce a sanadiyyarsa APC ta lashe zaben 2015 da 2019 a Najeriya.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an san tsohon abokin takarar na Muhammadu Buhari a CPC da sukar Bola Tinubu, sai kuma aka ji yanzu ya na jinjina masa.

A wani jawabi da Fasto Bakare ya yi kwanan nan, ya kamanta ‘dan siyasar da Jephtaph na cikin Injila.Bakare ya kara wa tafiyar ta su Tinubu kwarin-gwiwa.

‘Dan siyasar ya yi kaca-kaca da ‘yan kwaratsin da ke sukar Tinubu duk da ba su kama kafarsa ba, amma ba su da aikin yi sai kokarin jefa zargi a kan nasabarsa.

Faston ya ce sanin sunan mahafiyar Asiwaju ko kuma mahaifinsa ba shi ne zai ceci Najeriya ba. “Duk da kalubale da gwagwarmayar da ya fuskanta a rayuwa, kamar dai Jephthah, ya hana jam’iyyar PDP iya taba Legas da jihohin yamma a 1999-2007.”

Bakare ya cigaba da cewa: “Idan za a fadi gaskiya, idan ba don hadin-kansa da kwarewarsa ba, da nasarar jam’iyyar APC a zabukan 2015 da 2019 ba zai taba yiwuwa ba.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here