Arewa: Gwamnonin Sun Shiga Taron Gaggawa
Gwamnonin jihohi arewacin kasar sun shiga wani taro na gaggawa yanzu haka – Suna taron ne a Sir Kashim Ibrahim House, da ke jihar Kaduna
Koda dai babu cikakken bayani game da ganawar tasu, ana ganin ba zai rasa nasaba da halin da kasar ke ciki ba a yanzu Labari da muke samu ya nuna cewa, a yanzu haka gwamnonin arewa sun garzaya jihar Kaduna domin yin wani taron gaggawa na kungiyarsu ta gwamnonin yankin arewacin kasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnonin jihohin arewa su 15 sun isa zauren kungiyar da ke Sir Kashim Ibrahim House, Kaduna da misalin karfe 1:55 na ranar yau Alhamis, 22 ga watan Oktoba. Bayan sun rero taken kasar, sai aka bukaci yan jarida da su fita domin gwamnonin su yi wata ganawa ta sirri.
Read Also:
Wasu daga cikin gwamnonin da suka isa taron sun hada da; gwamnan Filato kuma Shugaban kungiyar, Simon Bako Lalong, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal. Sai gwamnan jihar Gombe, Mohammed Inuwa Yahaya, gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq. Har ila yau gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni da kuma gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule duk sun hallara
A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jagorantar taron majalisar tsaro ta kasa a fadar Shugaban kasa da ke Abuja, a yau Alhamis, 22 ga watan Oktoba. Taron wanda ke gudana a kowani zangon shekara, na zuwa ne a yayinda ake tsaka da fuskantar tashe-tashen hankula a sassa daban-daban na kasar. Wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo, sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa, Ibrahim Gambari da kuma mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Janar Babagana Monguno. Har ila yau shugabannin tsaro da wasu daga cikin ministoci sun halarci taron.